2 Thessalonians 3

Roƙo don Adduʼa

1A ƙarshe, ʼyanʼuwa, ku yi mana adduʼa domin saƙon Ubangiji yǎ yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. 2Ku kuma yi adduʼa yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya. 3Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yǎ kuma tsare ku daga mugun nan. 4Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5Bari Ubangiji yǎ bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.

Gargaɗi game da Zaman Banza

6A cikin sunan Ubangiji Yesu, muna muku umarni, ʼyanʼuwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗanʼuwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar
Ko kuwa alʼada
da kuka karɓa daga wurinmu.
7Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza saʼad da muke tare da ku ba, 8ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. 9Mun yi wannan, ba don ba mu da ʼyancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. 10Ko ma a saʼad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa: “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

11Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. 13Game da ku kuma ʼyanʼuwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.

14In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yǎ ji kunya. 15Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗanʼuwa.

Gaisuwa ta Musamman

16Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yǎ ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yǎ kasance tare da ku duka.

17Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.

18Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ku duka.

Copyright information for HauSRK